Za'a soma binciken kisan Shugaba Juvenal Habyarimana

Shugaba Paul Kagame na Rwanda
Image caption Wasu alkalai da kuma masana shari'ar kasar Faransa zasu fara binciken kisan Shugaba Habyarimana na Rwanda

A yau Asabar ne wata tawagar alkalai da masanan shari'a na Faransa za ta fara bincike na tsawon makon guda a Rwanda kan kisan gillar da aka yiwa shugaba Juvenal Habyarimana shekaru sha shida da suka gabata.

A ranar shida ga Afrilun alif da dari tara da casa'in da hudu ne aka harbo jirgin da ke dauke da shugaba Habyarimana, abinda ya bude kofar kisan kare dangin da aka yi a Rwanda.

Alkalan na amfani ne da damar da ta biyo bayan sake kyautatar alaka tsakanin kasashen biyu bayanda binciken da Faransa ta fara a baya game da kisan ya sa Rwanda yanke huldar jakadanci da ita a shekarar dubu biyu da shida.