'Yan Nijar dake kasashen waje ba za su yi zabe ba

Shugaban mulkin sojin Nijar Salou Djibo
Image caption 'Yan Nijar dake kasashen waje ba zasu sami damar kada kuri'arsu a zaben shugabankasa mai zuwa ba

Al'umar jamhuriyar Nijar da ke zaune a kasashen waje ba za su jefa kuri'a ba a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Gwamnatin mulkin sojin kasar ce ta dau wannan mataki jiya a Yamai sakamakon wani taro karo na biyu da ministan cikin gida Dr Cisse Ousman ya yi da shugabannin hukumar zabe CENI da wakilan jam'iyun siyasan kasar.

A cewar hukumar zaben akwai matsaloli da take fuskanta da suka hada da rashin ingantacciyar rejista da kuma kudi da za su bada damar shirya zaben.

Sai dai ra'ayoyin 'yan siyasan sun sha bamban dangane da wannan mataki da gwamnatin ta dauka.