An kama fursunoni a Jos

Taswirar Najeriya
Image caption Rundunar hadin gwiwa ta samar da tsaro ta cafke fursononi biyu

A Najeriya,rundunar hadin gwiwa ta samar da tsaro a jihar Filato, ta ce ta kama fursunoni biyu da suka tsere daga gidan kurkukun Bauchi, sakamakon farmakin da wasu mutane da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai.

Rundunar ta ce ta sami narasar kama mutanen biyu sakamakon tsauraran matakan tsaro da ta dauka a jihar bayan labarin tserewar fursunonin na gidan yarin Bauchi.

Rundunar hadin gwiwar ta kuma bayyana cewa tuni ta mika wadannan mutane ga rundunar 'yan sandan Jihar Filato domin ci gaba da bincike.

A ranar talatar da ta gabata ne ,wasu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ce, suka farma gidan yarin na jihar Bauch, inda da dama daga fursunonin dake cikinsa suka tsere.