Za a gudanar da zanga zanga a New York

Shugaban Amurka,Barack Obama
Image caption Za a gudanar da zanga zanga a Amurka

Wasu kungiyoyi masu mabambantan ra'ayoyi na shirye-shiryen gudanar da zanga zanga a birnin New York na Amurka.

Kungiyoyin da za su gudanar da zanga zangar sune na masu nuna goyon baya da kuma masu adawa da shirin ginin cibiyar addinin musulunci a kusa da wurin da aka kai harin watan Satumbar shekarar 2001.

Masu nuna goyon baya ga gina cibiyar addinin musuluncin na shirin yin wani gangami a birnin Manhattan, don yin kira da a nuna kauna tare da mutunta juna.

Tun da farko wata mata dake halartar bikin a birnin New York ta ce abin da take bukata shi ne jama'a su zauna lafiya da juna.