Yau ake tunawa da harin 9/11 a Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Amurkawa na tunawa da hare haren ranar sha daya ga watan satumba a yau

A yau Asabar ne a Amurka ake tunawa da hare-haren sha daya ga watan Satumba, shekaru tara da suka wuce, inda aka kashe kimanin mutane dubu uku.

Batun gina cibiyar addinin Musulunci daura da inda aka kai harin a New York da kuma shirin nan da yanzu aka jingine, inda paston wani karamin choci a Florida ya dauri aniyyar kona alkur'ani mai tsarki ne za su fi jan hankulan jama'a a bana.

Da zarar an gama ayyukan tunawa da wannan rana sai kuma a fara zanga-zanga inda inda za'a yi gangamin goyon baya da kuma adawa ga shirin gina cibiyar addinin Musulunci hade da masallaci daura da wurin da aka fara kai harin.

Da alamun zagoyawar ranar a bana ita ce za ta kasance mafi rudani kawo yanzu.