Jami'an bankuna na taro a birnin Basel

An bayar da rahoton cewar manyan masu sa ido kan harkokin bankuna daga manyan kasashe masu arziki da kuma kasashe masu tasowa sun cimma yarjejeniya a kan sauye-sauye game da tsarin banki na duniya dake da nufin rage hadarin samun matsalar kudi a gaba.

Jami'an Bankin na yin taro ne a Birnin Basel na kasar Switzerland domin amincewa da sababbin dokokin dake da nufin kare bankuna a lokacin da suka yi asara ta yadda ba sai an ceto su da kudaden gwamnati ba,sannan kuma su sama musu kariya daga kamfar kudinsu.

Sauyi mafi muhimmanci zai yi kari a kan uwar kudin da ake bukata bankuna su tanada.

Wakilin BBC ya ce za a aika da wadannan shawarwari zuwa ga shugabannin kungiyar kasashe 20 da suka fi karfin tattalin arziki ta G20 domin su amince da su a wajen taron da za su yi a cikin watan Nuwamba.