Alkalan Faransa sun kai ziyara Rwanda

Paul Kagame
Image caption Paul Kagame

Wata tawagar alkalan Faransa da kwararru kan harkar shari'a sun isa Rwanda domin soma wani binciken sati guda game da kashe Shugaba Juvenal Habyarimana shekaru 16 da suka wuce.

Yunkurin ya biyo bayan gyaruwar dangantaka ne tsakanin kasashen biyu wadanda suka farfado da alakar diplomasiyya a bara.

Dangantaka ta tabarbare ne a shekara ta dubu 2006 bayan wani binciken Faransa na farko ya dora laifi a kan dakarun dake da alaka da Shugaban Rwanda mai ci Paul Kagame,da kashe Shugaba Habyarimana, wanda harbo jirginsa kasa a shekarar 1994, ya tayar da kisan kare dangi.