Amurka nada fatan Iran za ta saki wata Ba'amurka

Babban mai baiwa Shugaba Barack Obama shawara ya ce Amurka na cike da fata tare kuma da samun karfin guiwa daga bayanin Iran na aniyarta ta sakin wata Ba'amurkar da aka tsare a kusa da kan iyaka da Iraqi a cikin watan Yuli.

To amma Mashawarci, David Axelrod ya kara da cewar lamari ne na a jira a gani.

Tun farko wani mai gabatar da kara na Iran,Jafari Dowlata-badi, ya ce wata kotu ta baiwa matar, Sarah Shourd, beli mai dauke da sharadi na kusan dola dubu 500, saboda ba ta da lafiya.

An kama Ms Shourd ne tare da wasu Amurkawan maza biyu a cikin watan Yulin bara , aka kuma zarge su da leken asiri.

Amurkawan dai sunce suna balaguro ne, suka shiga cikin yankin kasar Iran bisa kuskure.