Gaskiya ce za ta ceto Najeria a zaben 2011

Masana akan harkar siyasa a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da cece- kucen da ake yi a game da wanda ya cancanci tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za'a yi a shekarar 2011.

A wata hira da Dakta Usman Muhammed na jami'ar Abuja ya yi da BBC, ya bayyana cewa hanya guda da za'a bi wajen kaucewa fadawa cikin halin rudani shine kowanne dan takara ya tsaya kan gaskiyarsa.

Ya kara da cewa ya kamata a kawar da akidar sai wane ko wane, 'yan Najeriya su mayar da hankulansu akan me 'yan takara za su yi wa kasa.

Ya yi misali da rigimar tsayawa takara da ke tsakanin Janaral Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Shugaba Goodluck Jonathan wanda dukansu 'yan jamiyyar PDP ne.

Kamar yanda Dakta Usman ya bayyana, idan har a cikin jam'iyya guda ana samun haka, to wannan ba zai haifar da komai ba illa rashin tabbaci da kuma rashin sanin inda aka dosa.

KARIN BAYANI

A 'karshen makon daya gabata ne dai chief Raymond Dokpesi shugaban 'kungiyar magoya bayan takarar Janaral Babangida, a wani taron manema labarai, ya yi zargin cewa fadar shugaban 'kasar na kulla makarkashiyar hallaka shi da kuma yunkurin durkusar da harkokin kasuwancin sa, saboda yaki amincewa ya goyi bayan shugaba Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasar a zaben dake tafe.

Sai dai tuni fadar shugaban 'kasar ta fitar da wata sanarwa inda ta musanta wannan zargi.