Erdogan yayi ikirarin nasara a kuri'ar raba gardama

Firayim Minista Recep Tayyip Erdogan
Image caption Firayim Minista Recep Tayyip Erdogan

Firayim minista Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya ce gwamnati ta samu nasara yadda ta kamata a kuri'ar raba gardama a kan wani jerin sauye sauye ga tsarin mulki.

Mr Erdogan ya ce kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna, sauye sauyen -- domin dakile ikon soji da kuma sakewa bangaren shara'a fasali -- sun samu kusan kashi 60 cikin dari na karbuwa.

Gwamnatin Turkiya ta yi ta cewar ana bukatar sauye sauyen domin karfafa demokuradiya.

To amma masu adawa na jin tsoron cewar za su baiwa Gwamnatin Erdogan, mai tushen siyasar Islama, matsananciyar damar fada aji a kan kotuna wadanda a wasu lokuta suke kalubalantar matakan da gwamnati ke dauka.