Cocin Belgium kan batun lalata da kananan yara

Archbishop  Andre- Joseph Leonard
Image caption Archbishop Andre- Joseph Leonard

Shugaban cocin Roman Katolika a Belgium ya amince cewa, wasu fada-fada da malamai, sun ci zarafin kananan yara masu yawa.

Archbishop Andre-Joseph Leonard ya ce, cocin na neman ba 'yan sanda hadin kai, domin a hukunta wadanda suka yi aika-aikar.

A makon da ya wuce ne, wata hukuma mai zaman kanta da cocin ta kafa, ta gano cewa, a shekaru da damaa da suka wuce, an ci zarafin kananan yara a kowane lardi da ke karkashin ikon bishop-bishop.