Kasar Cuba za ta zabtare yawan ma'aikatanta

 Raul Castro
Image caption Shugaba Raul Castro na Cuba

Kasar Cuba ta bada sanarwar shirinta na dakatar da kimanin kashi 20 cikin 100 na ma'aikatan kasar,wanda shi ne mataki irinsa na farko tun bayan juyin juya halin kasar a shekarar 1959.

Jamhuriyar Cuba ta ma'aikata, ta ce ma'aikata kimanin dubu dari biyar ne za su rasa aikinsu cikin watanni kalilan dake tafe, kuma a karshe ma guraben aiki miliyan ne za a yi asara.

Wakilin BBC ya ce ma'aikatan da aka dakatar, za a ba su kwarin gwiwar kirkiro da sana'o'i domin cin gashin kansu, ko kuma su shiga aiki a kananan masana'antu masu zaman kansu.

Kadan ne daga cikin al'ummar kasar Cuba suke aikin dogaro da kansu, kuma da alamu tattalin arzikin kasar na cikin wani hali na tsaka mai wuya.