Ta yiwu a sake tumbuke Prim Minista a Japan

Image caption Naota Kan

Bisa ga dukkan alamu kasar Japan zata sauya Piram Minista a karo na uku, cikin shekara guda.

A yau ne dai jam'iyya mai mulkin kasar, ta Democratic Party, za ta kada kuri'a akan ko zata tumbuke Piram minista mai ci, wato Naoto Kan.

Shi dai Mista Kan, ya na fuskantar kalubale ga shugabancinsa na jam'iyyar ne daga wani gogaggen dan siyasa a kasar mai suna Ichiro Ozawa.

BBC dai ta fahimci cewa ko ma waye ya samu nasara a wannan karawa da za'a yi, to zai fuskanci kalubale da dama.

Daga cikinsu kuwa sun hada da batun tashin da darajar kudin kasar wato Yen ke yi, wanda 'yan kasuwa suka ce yana kawo musu koma baya.