An yiwa wasu mutane 'yan gida guda kisan gilla a Kano

Masu ta'aziyya a Kano
Image caption Masu ta'aziyya a Kano

A Kano an yi jana'izar wasu mutane biyar, 'yan gida guda, wadanda aka kashe a daren jiya.

Wasu mutane ne da ba a shaida ko su wanene ba suka shiga wani gida, a rukunin gidajen dake unguwar Kundila dake kan titin Gidan zoo, a cikin birnin Kano, inda suka yanka wani magidanci mai suna Garba Bello, mai kimanin shekaru hamsin da biyar, tare da matarsa da kuma 'ya'yansa ukku. Marigayi Garba Bello, mataimakin darakta ne a hukumar 'yansandan ciki ta Nigeria, wato SSS, wanda ke aiki a Sakkwato.

Rundunar 'yan sandan Kanon ta ce, kisan ba shi da nasaba da aikin fashi da makami, ya fi kama da kisan gilla.