An kashe mutane sha takwas a zanga zangar Kashmir

Mutane akalla 18 ne suka rasu sannan kimanin dari suka jikkata bayanda wata zanga zanga da ta barke, ta haddasa rikici a Kashmir dake karkashin ikon kasar India.

Yan sandan kasar India sun bude wuta kan dubban masu zanga zangar wadanda suka hau kan tituna domin bayyana kin jinin mulkin kasar India a yankin.

Haka kuma suna nuna kyama ga wani rahoton da kafar talabijin a yankin ya watsa cewa an wulakanta Alqur'ani mai tsarki a Amurka.

Masu zanga zangar cikin fushi, sun kona mutum mutumin shugaba Obama, sannan suka rika kururuwar nuna kin jinin Amurka.