An fara manna pastocin 'yan takara a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, a manyan titunan birane da kauyuka, an fara manna hotunan wasu masu neman jam'iyyunsu su tsayar da su takara.

Wannan dai ya biyo bayan damar soma yakin neman zabe a matakin jam'iyya da hukumar zaben kasar wato INEC ta bai wa jam`iyyun siyasa.

To sai dai wani kalubalen da siyasa a Najeriya ke fuskanta shi ne yadda yakin neman zaben zai gudana ba tare da wata husuma ta tashi ba.

Ana zargin wasu 'yan siyasar cewa su kan yi amfani da 'yan banga, ko miyagu domin cimma wasu manufofinsu na son zuciya, inda wani lokaci ma har akan rasa rayukan jama`a.

To sai dai kuma wani Sanata a Najeriya ya yi bayanin hanyoyin da za'a bi domin gujewa rigingimun siyasa da aka fuskanta a baya.

A cewar Sanata Abubakar Sodangi, ya kamata 'yan siyasa su yarda da cewa mulki na Allah ne.

Ya kara da cewa ya kamata a guji lalata rayuwar matasa da sunan bangar siyasa.

Sanata Sodangi dai ya ce ya kamata siyasar Najeriya ta tafi da zamani, kamar yanda a ke yi a kasashen da suka cigaba.