Najeriya za ta yi afuwa ga masu satar mutane

A Najeriya, hukumomin shiyyar Kudu maso Gabashin kasar na shirin fito da wani tsari na yin afuwa ga masu garkuwa da mutane domin neman fansa a jihohin shiyyar.

Hukumomin dai sun bayyana cewa wannan shirin yin afuwar, tare kuma da matakan tsaron da ake dauka za su taimaka wajen shawo kan matsalar.

A yanzu haka, har ma an kafa wani kwamiti na musamman da ya kunshi sojoji da 'yan sanda da duk wasu masu fada a ji a yankin, domin fara aiwatar da shirin afuwar.

Wannan dai ya biyo bayan kara yawaitar fashi da makami da sace mutane ana garkuwa da su da zummar sai an biya kudin fansa.

A don haka ne ake kokarin kaddamar da shirin yin afuwar ga masu aikata wannan miyagun laifukan muddin za su saduda.

Za kuma a fara ne daga jihar abia, kana daga bisani a yi a sauran jihohin shiyyar.

A bara ne dai aka fara kaddamar da irin wannan shirin na yin afuwa ga masu gwagwarmaya da makamai a yankin Naija Delta, domin shawo kan matsalar sace- sacen jama'a ana garkuwa da su domin neman kudin fansa, da dai sauran miyagun laifuka.