Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na ziyara a Nijar

Wakilin majalisar dinkin duniya mai kula da Afrika ta yamma, Mista Said Djinnit, ya ce ya gamsu da shirye-shiryen da ake na mayar da Nijar bisa tafrakin demokradiyya.

Ya bayyana hakan ne, a lokacin ganawar da ya yi yau din nan a birnin Yamai, tare da shugabannin siyasar kasar ta Niger.

Baya ga batun zaben, mahalarta taron sun kuma duba matsalar abincin da ake fama da ita a kasar, da kuma maganar tsaro a yankin Sahel.

Mr Djinnit ya gana da Shugaban kasar Nijar, Janar Salou Djibo, wanda ya yaba mawa kan kokarinsa na mayar da kasar kan tafarkin demokuradiya da kuma tinkarar matsalar karancin abincin da aka fuskanta.

Jami'in na Majalisar dinkin duniya ya kuma yi tozali da Shugabannin Hukumar zabe mai zaman kanta, CENI don jin halin da ake ciki game da shirye-shiryen zaben dake tafe a kasar.