Fidda gwani na jamiyyar republican ta Amurka

A Amurka, alamu na bayyana cewa wadanda ke sahun gaba a jam'iyyar Republican ta kasar, sun samu koma baya a zagayen karshe na zabukan fidda 'yan takara.

An yi wannan zaben ne a gabanin zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za'a yi cikin watan Nuwamba mai zuwa.

A jihar Delaware 'yar takarar gamayyar jam'iyyun nan ta Tea Party, Christine O'Donnell ce ta lashe zaben fidda dan takarar majalisar dattawa na jam'iyyar ta Republican.

Jihar Delaware dai ta zama tamkar wani fage ne na kece-raini a cikin jam'iyyar Republican, musamman ma tsakanin 'yan mazan jiya da kuma sabbin jini.