Iran ta bada belin 'yar Amurka

Sarah Shourd
Image caption Sarah Shourd

Rahotanni daga Tehran na nuna cewa gwamnatin Iran ta bada belin ba'amurkiyar nan Sarah Shourd, wadda aka kama a bara tare da abokan tafiyanta, bayanda suka tsallaka iyakar Iran ba tare da takardun izinin shiga kasar ba.

An zargi Ms Shourd da sauran Amurkawan guda biyu da laifin leken asiri, kuma an tsare su a gidan yarin Evin dake babban birnin kasar ta Iran na tsawon fiye da shekara guda.

Dukkanin mutane ukkun sun hakikance cewa sun shiga Iran ne bisa kuskure a lokacin da suke yawon bude ido a Iraqi.

Masu gabatar da kara sun fadi a ranar Lahadi cewa Miss Shourd wadda ke fama da rashin lafiya, ka iya samun yanci idan aka biya belin dala dubu 500.