Akalla mutane dubu goma na gudun hijira a Kebbi

Image caption Ambaliyar ruwa

Hukumomin jahar Kebbi sun ce, akalla mutane dubu goma ne suka shiga gudun hijira, sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a karshen makon jiya.

Wannan dai ya biyo bayan fashewar wata madatsar ruwa a makwabciyar jahar Sakkwato.

A cewar hukumomin kuma, ruwan ya lalata dubban hectoci na shinkafa, da kuma gadoji akalla hudu.

Hakan na faruwa a daidai lokacin da kuma ake fargabar cewa, ruwan da ke cigaba da kwarara zuwa kuryar jahar ta Kebbi, zai iya jefa wasu dimbin mutanen cikin mawuyacin hali.