Bayan samun ‘yancin kai

Image caption Sir Ahmadu Bello

Bayan shafe shekara da shekaru ‘yan kishin Najeriya na ta gwagwarmayar kwatowa kasar ‘yanci kai daga Turawan mulkin mallaka na Burtaniya, a karshe hakarsu ta cimma ruwa, inda ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda ya zamo Fira ministan Najeriya na farko ne ya karbi tutar ‘yancin kasar daga hannun gwamna janar Sir James Willson Robertson, wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 1955-1960.

An gudanar da zaben farko a Najeriya a shekarar 1959, ko da yake jam'iyyar NPC ta Arewa ita ce ta fi samun kuri'u a zaben, to amma yawan kuri'un da ta samu basu isa ta kafa gwamnati ba, abinda yasa ta kafa gwamnatin hadin gwuiwa tare da jam'iyyar NCNC ta kabilar Ibo.

Bayan da kasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960, wadannan jam'iyyun biyu ne suka kafa gwamnati, inda bisa tsari Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya kamata ya zama Fira minista, amma sai ya marawa mataimakinsa baya wato Sir Abubukar Tafawa Balewa wanda ya zamo Fira ministan farko, shi kuma Dr. Nmandi Azikwe gwamna janar na farko a Najeriya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A daya bangaren kuma jam'iyyar Action Group ko AG ta Yarabawa, wadda Obafemi Awolowo ya jagoranta ta kasance jam'iyyar adawa.

Akwai banbance-banbancen addini da al'adu sosai tsakanin Hausawa a Arewaci, Ibo a Gabashi da Yarabawa a kudancin kasar.

An yi ta samun rikice rikice a gwamnatin hadin gwuiwar wanda ya kai ga rarrabuwar kai tsakanin wadanda ke cikin gwamnatin.

Ita ma jam'iyyar adawa ta AG ta samu rarrabuwar kai tsakanin 'ya 'yanta, inda a shekarar 1962 wani bangaren jam'iyyar ya ware ya kafa wata sabuwar jam'iyya mai suna Nigerian National Democratic Party (NNDP), wadda S. I. Akintola ya jagoranta.

Image caption Sir Abubakar Tafawa Balewa

Rigingimun siyasa sun mamaye gwamnatin wannan lakoci, abinda ya kai ga kafa yankin yamma ta tsakiya wato Mid-Western region a shekarar 1963 daga cikin yankin yammacin kasar.

Ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1963 ne aka amince da kundin tsarin mulkin kasar kuma a wannan lokaci Najeriya ta zama mamba a kungiyar kasashen renon Ingila ko Commonwealth Kundin tsarin mulkin yasa Najeriya ta koma ga tsarin mulkin tarayya dake da shugaban kasa da mataimakinsa, inda aka zabi Dr Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban tarayyar Najeriya.

A shekarar 1963 an gudanar da kidayar jama'a wanda ya nuna yankin Arewa ne ya fi kowane yanki yawan jama'a a kasar.

Sakamakon kidayar ya jawo rikici tsakanin yankunan Najeriya, inda jam'iyyar NCNC ke ganin an yi hakanne domin kawai a ba yankin Arewa kujeru mafi yawa a majalisar dokokin kasar.

Bayan da rigingimun suka ki ci suka ki cinyewa, sai sojoji suka yi juyin mulkin farko a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966.