Masana kimiyya sun gano hanyar gwajin cutar TB

Image caption Mai dauke da cutar tarin fuka

Masana ilimin Kimiyya a Birtaniya sun fito da wani nau'in gwaji da zai iya gano kwayar cutar tarin fuka ko TB a cikin sa'a guda.

Kungiyar lafiya ta Health Protection Agency dai ta bayyana cewa gwajin zai iya gano duk wata alama ta kasancewar kwayar halittar da ke haddasa cutar, komai kankantar ta.

Kamar yanda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, a shekarar 2008, fiye da mutane miliyan daya ne dai a duk fadin duniya suka rasu a sanadiyar cutar TB.

Sannan kuma kiyasi na nuni da cewa kimanin kashi daya cikin uku na al'ummar duniya na dauke da kwayar halittar dake haddasa cutar tarin fuka ko TB.

Sai dai kuma kamar yanda bincike ke nunawa, kashi biyar zuwa goma cikin dari na masu dauke da kwayar halittar ne ke kamuwa da ainihin cutar.

Sai dai duk da haka, wannan na janyo asarar miliyoyin rayuka.

Gano masu dauke da kwayar halittar dake haddasa cutar dai na da wahalar gaske.

Za'a iya shafe tsawon makwanni takwas kafin a iya ganowa, wanda kafin nan, mai dauke da ita ya yadawa mutane da dama.

A Birtaniya masana ilimin kimiyya yanzu dai sun gano wata hanyar da za'a iya ganin alamun kasancewar kwayar cutar ba tare da daukar lokaci mai tsawo ba.

Kuma an gano wannan sabuwar hanyar ne a daidai lokacin da cutar ke kara bazuwa, inda ta kan janyo asarar dimbin rayuka.