An samu raguwar masu yunwa a duniya

Yawan mutanen da ke fama da yunwa a duniya ya ragu, a karon farko a cikin shekaru goma sha biyar.

Wasu alkalumman da ba a dade da wallafawa ba, a ofishin majalisar dinkin duniya a birnin Rome sun nuna cewa, yawan mutanen da basu samun isasshen abinci ya dan zarta miliyan dari tara, idan an kwatanta da shekarar da ta wuce, inda yawansu ya dara biliyan guda.

An dan sami cigaban ne, saboda kyautatuwar tattalin arziki, da kuma damina mai albarka.

Sai dai a cewar shugaban hukumar samar da abincin majalisar dinkin duniya, har yanzu ana fuskantar bala'in yunwa.