Zaben shekarar 1993

Mashood Abiola
Image caption Marigayi Cif Moshood Abiola ne na jam'iyyar SDP ake kyautata zaton cewar ya lashe zaben shugaban kasar

Domin cika alkawarin daya dauka na mika mulki ga farar hula, jagoran mulkin soji na lokacin janar Babangida ya baiwa 'yan siyasa damar kafa jam'iyyu wadanda hukumar zabe taiwa rijista, inda ta bayyana cewa ranar 24 ga watan Janairun shekarar 1992 za'a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu.

Sai dai kuma kafin wannan lokacin, janar Babangida ya rushe dukkan jam'iyyun da aka kafa, inda ya kafa jam'iyyu biyu wato SDP da NRC, kuma ya bukaci dukkan 'yan Najeriya dake sha'awar shiga jam'iyyun su shiga.

A watan Apirilun shekarar 1993 jam'iyyar SDP ta zabi Moshood Kashimawo Olawale Abiola wato MKO, a matsayin dan takarar shugaban kasarta, ita kuma jam'iyyar NRC ta zabi Bashir Tofa a matsayin nata dan takarar shugaban kasa.

Ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993, aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda aka ki bayyana dukkanin sakamakon zaben, duk kuwa da cewa an bayyana na wasu jihohin, wanda ya nuna cewa Abiola ya lashe jihohi 19 daga cikin talatin, abinda ya nuna cewa shi ne ya yi nasarar zaben.

Kamar yadda aka shirya an gudanar da zaben, inda jam'iyyar SDP tai nasara da gagarumin rinjaye a majalisun dokokin kasar, sai dai kuma a ranar 7 ga watan Agustan shekarar 1992 aka soke zaben share fage na shugaban kasa bisa zargin magudi.

Rashin bada dalilan soke zaben ya jawo tashe tashen hankula a sassa daban-daban na Najeriya, musamman a yammacin kasar inda daga nan ne Cif MKO Abiola ya fito.

Ranar 26 ga watan Agustan shekarar 1993, janar Babangida ya bayyana batun saukarsa daga kan mulki inda ya mika ragamar mulkin ga gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Cif Ernest Shonakon.

Watannin uku da kafa gwamnatin rikon kwaryar sai wasu sojojin karkashin jagorancin janar Sani Abacha suka yi juyin mulki.