Juyin mulkin shekara ta 1985

Image caption Ba zub da jini ba a juyin mulkin

Ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1985, sojoji karkashin jagorancin janar Ibrahim Badamasi Babangida suka hambarar da gwamnatin janar Muhammadu Buhari a wani juyin mulkin da ba'a zubda jini ba.

Babban dalilin da sojojin suka bayar na hambarar da gwamnatin janar Muhammadu Buhari shi ne na dagewar da yayi na cewa sai ya gudanar da bincike a ma'aikatar tsaron kasar game da zarge-zargen da ake na wasu kwangiloli da aka bayar a ma'aikatar.

Wasu na ganin da a ce an gudanar da bincike to kuwa da an samu dayawan manya-manyan sojojin da hannu, wadansu sune suka hada juyin mulkin.

Janar IBB kamar yadda ake kiransa ya hau mulkin da zummar kawo karshen take hakkin bil'adama da ake zargin gwamnatin Buhari da yi tare kuma da mika mulki ga farar hula a shekarar 1990.

Image caption Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Sai dai kuma wasu na ganin take hakkin dan adam din ya ma fi kamari a lokacin mulkinsa.

A lokacin mulkin janar Babangida aka kaddamar da shirin tada komadar tattalin arziki wato Structural Adjustment Program ko SAP a takaice a shekarar 1986, kamar yadda hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF da Bankin Duniya suka ba gwamnatin shawarar yi domin farfado da tattalin arzukin kasar.

Kuma wannan shiri a iya cewa yayi tasiri tsakanin shekarar 1986 zuwa da 1988 a lokacin da aka samu bunkasar tattalin arziki.

A lokacin mulkin janar Ibrahim Badamasi Babangida ne Najeriya ta zama cikakkiyar mamba a kungiyar kasashen musulmi wato OIC.

Ranar 22 ga watan Aprilun shekarar 1990 wasu sojoji karkashin jagorancin Manjo Gideon Orkar sukai kokarin kifar da gwamnatin IBB.

A lokacin da sojojin suka yiwa fadar shugaban kasar kawanya, janar Babangida yana ciki, amma dai ya samu ya sulale ta wata barauniyar hanya ta bayan gidan.