An bayana sakamakon binciken mutuwar Bibi Ngota

Samakon farko na binciken da Shugaban kasa Paul Biya ya nemi a gudanar dangane da mutuwa a gidan yari da Bibi Ngota, Editan jaridar "Cameroon Express" ya yi a watan Afrilu ya fito.

A rahoton da Prime Minista, kuma Ministan shari'a Amadou Ali ya gabatar, ya nuna cewa dan jaridan ya mutu ne a dalilin wasu cututtuka kamar kanjamau, da kaba, hadi da hawan jini, a maimakon gallaza masan da aka ce anyi lokacin da yake hannun jami'an tsaro.

Bibi Ngota ya shiga hannun 'yan sandan gudanar da bincike ne a ranar 10 ga watan maris na wannan shekarar bayan an tuhume shi da laifin mallakar wata takardar sirri da ya wallafa, kuma ya gurbata labarin da yake ciki.