Gwamnatin rikon kwarya

Ernest Shonekan
Image caption Ernest Shonekan

Ranar 26 ga watan Agustan shekarar 1993 ne janar Ibrahim Badamasi Babangida ya rantsar da Cif Erenest Shenekon a matsayin shugaban rikon kwarya.

Wannan shi ne mataki na karshe da janar Babangida ya yi niyyar dauka kafin mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Tattalin arzikin Najeriya a wannan lokaci ya ja da baya, wanda bayan hawansa, Cif Ernest Shenekon ya yi ta kama kafar kasashen dake bin Najeriya bashi na su yafe mata.

Sai dai kuma soke zaben su Abiola, yasa yawancin kasashen yammaci sun juyawa Najeriya baya inda aka yi ta kakaba mata takunkumi.

Jama'ar yankin yammacin Najeriya wato yankin da Cif Shenekon ya fito sun dauke shi a matsayin wanda ya hana ruwa gudu a kokarin tabbatarwa da MKO Abiola zaben da ya ci.

Babban aikin da Cif Shenekon ya fara bayan hawansa mulki shi ne na sakin 'yan siyasar da aka tsare kuma ya bada ranar da za'a janye dakarun Najeriya dake aiki a karkashin ECOMOG a Laberiya.

Rashin tasirinsa sosai kan sojin kasar a karshe ya kai shi ya baro. Domin kuwa sakataren tsaron da aka rantsar ran 26 ga watan Agustan 1993 shi ne ya hambarar da gwamnatinsa a watan Nuwambar wannan shekarar, wato watanni uku da hawan gwamnatin.