An zargi wani matashi da kashe mahaifansa a Kano

'Yan sandan Nijeriya
Image caption 'Yan sandan Nijeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta samu Bello Garba babban da ga jami'in hukumar 'yan sandan ciki wato SSS, Garba Bello da zargin kisan mahafin nasa da matarsa da 'ya'yansa uku ciki har yarinya mai shekaru biyar.

Kwamishinan 'yan sandan jahar ta Kano Muhammad J. Gana ya shaidawa taron manema labarai a Kano cewa tun bayan kisan gillar da aka yiwa mutanen suka dukufa wajen bincike, kuma bayanan da suka samu na farko-farko su ne suka sa suke tuhumar wanda ake zargi da aikata kisan, wanda kuma a cewarsu yau ya tabbatar musu da zargin da suke masa.

A daren litinin din da ta gabata ne dai aka wayi gari wasu da ba'a san ko su wane ne ba sun kashe mutanen biyar 'yan gida guda, kuma babu wanda ya yi saura sai babban dan mai gidan da kuma daya daga cikin 'ya 'yansa wanda akace ya buyane a bandaki.