Majalisar Dinki Duniya ta ce mace-macen mata ya ragu

Kungiyoyin bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun ce yawan mace-macen mata wajen haihuwa ya ragu da kimanin kashi daya bisa uku tsakanin shekarun 1990 zuwa shekara ta 2008.

Ko da yake dai hakan za'a iya cewa tamkar wani albishir ne, amma majaliar dinkin duniyar ta ce wadannan al'kaluma sun nuna cewa zai yi wuya a cimma muradun majalisar dinkin duniya na rage mace-macen mata wajen haihuwa da kashi uku cikin hudu da ga nan zuwa shekara ta 2015.

Sannan kuma yunkurin samun kiwon lafiya ga kowa da kowa zai yi wuyar samu.

A shekarar 1990, majalisar ta kiyasta cewa mata dubu dari biyar da arba'in da shida ne ke mutuwa yayin haihuwa.

Zuwa shekarar 2008, adadin ya ragu zuwa dubu dari uku da hamsin da takwas.

Abin gwanin ban sha'awa! Sai dai kuma kash! Har yanzu kimanin mata dubu guda ne ke mutuwa a kowace rana a yayin haihuwa, mafi yawansu kuma a kasashen nahiyar Afrika ta kudu da Sahara da kuma kudancin Asiya.