Takaitaccen tarihin janar Mohammadu Buhari

Janar Mohammadu Buhari
Image caption Janar Mohammadu Buhari

An haifi Janar Muhammadu Buhari ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura.

Tauraruwar janar Buhari ta fara haskawa a lokacin da aka bashi mukamin ministan man petur da ma'adanai a shekarar 1975, a zamanin mulkin sojin janar Olusegun Obasanjo.

Ko da yake kafin nan shi ne gwamnan sabuwar jahar Arewa maso Gabas da janar Murtala Ramat Muhammed ya kirkiro.

Daga bisani kuma aka nada shi shugaban hukumar NNPC wadda aka fara kafawa a shekarar 1977.

A zamanin mulkin Janar Sani Abacha an nada shi shugaban hukumar PTF wadda aka kafa da kudaden rarar man da kasar ta samu a wannan lokaci domin gudanar da ayyukan ci gaban al'umma.

Kuma ayyukan da janar Buhari yayi wa Najeriya kama daga hanyoyi, asibitoci zuwa makarantu yasa wasu 'yan Najeriya son ganin ya sake zama shugaban kasar.

Sau biyu janar Muhammdu Buhari yana tsayawa takarar shugaban kasar karkashin tutar jam'iyyar ANPP wato 2003 da 2007, wadanda duka bai samu nasara ba.

Rashin nasarar da ya yi karo biyu bai sauya masa ra'ayi ba game da siyasa a Najeriya, kuma tuni ya kaddamar da tashi jam'iyyar da ya kira CPC wadda yake takarar shugaban kasa a zaben da za'a yi a shekarar 2011.