Me baiwa Paparoma shawara ya fasa zuwa Birtaniya

Paparoma Benedict da Archbishop William
Image caption Paparoma Benedict da Archbishop William

Daya daga cikin manyan masu baiwa Paparoma shawara ya ce ba zai raka Paparoman zuwa Birtaniya ba a ziyararsa mai tarihi wadda zai fara a ranar Alhamis.

Sanarwar ta sa ta biyo bayan wallafa wata hira ce da aka yi inda aka rawaito mai bada shawarar wato Cardinal Walter Kasper, yana yin wasu kalamai na rashin gamsuwa a game da kasar ta Birtaniya.

Cardinal Kasper ya ce Birtaniya ta yi kama da kasa mai tasowa, saboda irin yadda take bayyana tsauttsauran ra'ayin rashin addini.

Majalisar Mujami'ar Katolika ta Vatican ta ce cardinal din ya fasa ziyarar tare da Paparoman ne saboda rashin lafiya.