Ghana ce ta farko da za ta rage talauci a Afrika

Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills
Image caption Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills

Wata cibiya mai gudanar da bincike kan ci gaban kasa da kasa ta yi hasashen cewa Ghana ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da zata iya rage talauci zuwa rabi daga nan zuwa shekara ta 2015.

Wannan cibiya mai suna the Overseas Development Institute a turance, ta ce a shekarar 1990 rabin mutanen kasar Ghanan suna fama da talauci, amma yanzu alkaluman sun ragu zuwa rubu'i.

Sirrin da kasar Ghana ta bi, na iya cimma burin muradun karnin dai shine maida hankali da ta yi akan aiki gona, bangare da lokuta da dama gwamnatocin kasashe da dama da kuma kungiyoyin bada agaji ke mantawa da shi.

A sakamakon sauye sauyen da take yi da gine ginen tituna da kuma shirye shiryenta na hakar zuba jari yasa bangaren aikin gonar kasar ya bunkasa.