An dage zaben shugaban kasa a Guinea

Wani dan kasar Guinea yana kada kuri'a
Image caption Wani dan kasar Guinea yana kada kuri'a

Hukumar zabe ta kasar Guinea ta bayyana cewa za a dage zagaye na biyu na zaben shugaban kasar wanda aka shirya gudanarwa ranar Lahadi saboda rashin kammala shirye-shiryen zaben.

Wani mai magana da yawun hukumar zaben ta Guinea ya shaidawa BBC cewa ana bukatar karin lokaci don shiryawa zagaye zaben.

Thierno Ceydou Bayo ya ce babu takardun zabe fiye da dubu dari hudu da sittin wadanda ake sa ran za su isa kasar daga Afirka ta Kudu da yammacin ranar Lahadi mai zuwa.

Kuma za a dauki lokaci mai tsawo kafin a kai takardun yankunan karkara inda mutane ba su samu damar yin zaben zagaye na farko ba.

Don haka ne, a cewar Mista Bayo, ake bukatar jinkiri na makwanni biyu.

Ya kuma kara da cewa yau Alhamis za a bayyana sabuwar ranar gudanar da zaben, bayan wata tattaunawa tsakanin hukumar zaben da Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar.

A karshen makon da ya gabata dai rikici ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan siyasa masu adawa da juna, ya kuma haddasa mutuwar mutum guda yayin da wadansu mutanen akalla hamsin suka yi rauni.