Mexico na cika shekaru 200 da samun 'yanci

Bukukuwan samun 'yancin kai a Mexico
Image caption Bukukuwan samun 'yancin kai a Mexico

A kasar Mexico, dubban jama'a ne suka fito kan titunan kasar inda suke bukukuwan cikar kasar shekaru dari biyu da samun 'yancin kai daga kasar Spaniya.

A birnin Mexico City inda aka tsaurara matakan tsaro fiye da yadda aka saba, dubban jama'a ne suka fito don kallon faretin da ake yi wanda ya ratsa manyan tituna inda ake ta wasan wuta.

Shugaban kasar Felipe Calderon yayi ta jinjinawa dubban jama'ar da suka fito don gudanar da bukukuwan wannan rana.

Gwamnatin kasar dai ta sha alwashin gudanar da gagarumin buki duk kuwa da cewa wadansu mutanen kasar na ganin gudanar da bukin ba shi da wani muhimmanci ga kasar wadda ke cikin halin matsin tattalin arziki, ta ke kuma fama da gungun masu fataucin miyagun kwayoyi.