An sace wasu ma'aikatan kamfanin Areva a Nijar

Shugaban mulkin sojin kasar Nijar Salou Djibo
Image caption An sace wasu ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinan kasar Faransa mai suna Areva su bakwai a yankin Agadez na arewacin Nijar

Wasu masu dauke da makamai da ba a tantance ko su wanene ba sun sace wasu ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinai na kasar Faransa mai suna Areva su bakwai a cikin daren jiya a Yankin Agadez na arewacin kasar Nijar.

Mutanen dai sun hada da ma'aikata biyar haifaffun kasar Faransa da wasu 'yan Afirka guda biyu .

Yankin sahel wanda ya hada da arewacin Nijar da Mali dai ya kasance wani yanki inda ake zargin wasu kungiyoyi da sace sacen mutane.

Kawo i yanzu dai, hukumomin kasar Faransa sun ce suna ci gaba da bin kadin wannan lamari