Tasirin jadawalin zabukan jam'iyyar PDP

Dakta Okwesileze Nwodo
Image caption Shugaban jam'iyyar PDP, Dakta Okwesileze Nwodo

Jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta fitar da jadawalin zabenta na fid da gwani, wanda wadansu ke ganin sakamakon matsin lamba ne daga gwamnonin kasar da ke jam’iyyar.

Sai dai jam’iyyar ta musanta hakan.

A wani zaman gaggawa da Majalisar Zartarwar jam’iyyar ta gudanar jiya, ta amince cewa za ta fara ne da zaben ’yan majalisun dokoki na jihohi da gwamnoni kafin ta yi na ’yan majalisun dokoki na kasa da kuma shugaban kasa.

A bisa wannan tsarin, jam’iyyar za ta gudanar da zaben fid da gwani na ’yan majalisun dokoki na jihohi ranar 2 ga watan Oktoba; na gwamnaoni kuma 6 zuwa 8 ga watan na Oktoba.

An kuma tsara yin zabukan fid da gwani na ’yan majalisun dokoki na kasa daga ranar 12 zuwa ranar 15 ga watan Oktoba, yayinda za a kammala da na shugaban kasa daga ranar 18 zuwa 20 ga watan na Oktoba.

Wannan tsari dai ya saba da tsarin Hukumar Zabe mai Zaman kKanta ta kasar wadda ta tsara zaben ’yan majalisun dokoki na kasa da na shugaban kasa ya gabaci na gwamnoni.

Wadansu masana harkokin siyasa na fassara hakan da cewa gwamnoni ne suka yi amfani da karfinsu da kuma yawansu don ganin karfin fada-a-jin da suke da shi bai saraya ba.

A cewar Dakta Kabir Mato, wani malami a Jami’ar Abuja, a yunkurin da ’yan majalisun dokoki na kasa suka yi don tauye tasirin gwamnonin, sun yi tuya sun manta da albasa.

“Abin da ’yan majalisun suka yi a [gyaran] dokokin zabe na 2010 (cewa a fara zabukan daga na ’yan majalisun dokoki na kasa da na shugaban kasa kafin na gwamnoni), bai ma gwamnoni dadi ba.

“Shi ne su kuma suka yi amfani da karfin da suke da shi a jam’iyya da yawansu suka tursasawa jam’iyya a kan cewa tunda wancan ya zama doka, babu yadda za su yi da shi, to yanzu su ma suna da dama [tunda] ’yan majalisa ba su yi dokar cewa jam’iyyu ma dole [haka] za su gudanar da zaben fid da gwani ba”.

Sai dai jam’iyyar ta ce ta dauki wannan mataki ne bisa radin kanta.

A cewar mataimakin shugaban jam’iyyar a shiyyar arewa maso yammacin kasar, Dakta Danladi Abdullahi Sankara, “Ko wacce jam’iyya tana da ka’idojinta; ita PDP ka’idojinta ke nan, wannan tsari ne na PDP, haka muke so, haka kuma muka zana....

“Koma dai menene ba abin da ya damu kowa ba ne—gwamnonin da ake magana Allah Ya sa duk ‘yan jam’iyyar PDP ne; mun hadu mun daidaita, tsari ya tafi mana daidai, don haka ba maganar cewa wannan gwamna ne wannan ba gwamna ba ne”.