Fafaroma na ziyara Burtaniya

Image caption Fafaroma da sarauniya Elizabeth

Fafaroma Benedict ya yi kira ga Burtaniya kada da ta manta da asalinta na kiristanci, a yayin da take kokarin zama kasa mai al'umma daban-daban.

Lokacin da yake magana a Edingburg, babban birnin Scotland Fafaroma Benedict ya ce yancin da ake da shi a Birtaniya yana da tushe ne daga kiristanci, abinda kuma yanzu masu tsaurin raba addini da mulki suke adawa da shi.

Fafaroma Benedict ya ce yadda akai ta samun bayanan dake nuni da yadda limaman coci coci suke lalata da kananan yara abun ya tayar masa da hankali kwari da gaske

Ya kara da cewa abin bakin ciki shine ganin cewar hukumomin coci ba su sa ido sosai ba ga al'amarin kuma basuyi gaggawar daukar matakin da ya dace.