Talauci na karuwa a Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Adadin Amurkawa da ke rayuwa cikin talauci ya karu da kusan miliyan hudu a shekarar farkon mulkin shugaba Obama.

Wasu alkaluma da gwamnatin Amurka ta fitar na nuna cewa adadin Amurkawa da ke rayuwa cikin talauci ya karu da kusan miliyan hudu a shekarar farkon mulkin shugaba Obama.

Alkaluman shekarar 2009 da hukumar kidayar kasar ta fitar ya nuna cewa a cikin shekaru uku a jere, talauci na cigaba da karuwa a kasar.

Hukumar ta kuma ce wannan shi ne mafi yawan karuwar matalauta da aka samu tun shekarar 2004.

Abu mafi damuwa shine alkaluman da aka fitar sunyi nuni da cewar sai a watan daya gabata ne masu gidaje amurkawa da dama suka soma murmurewa daga rikicin tattalin arzikin daya taba su, fiye da kowane lokaci tun daga lokacin da rikicin tattalin arzikin ya kunno kai.