Jam'iyyar ANPP za ta yi babban taro na kasa

Tutar jam'iyyar ANPP

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, ANPP, ta ce zata yi babban taronta na kasa gobe Asabar don yin zaben fitar da dan takararta na mukamin shugaban kasa a zaben badi.

Jam’iyyar ta sanar da hakan ne bayan wani taron da jigoginta suka yi da kwamitin shirya babban taron.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rarrabuwar kawuna a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar, inda har wasu suka kori shugabannin jam’iyyar, kafin su ma daga bisani shugabannin su dakatar da su.

Jam’iyyar dai ta bayyana cewa ta dinke duk wata barakar da ke neman wargaza ta, sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu a tsakananin ’ya’yan nata.

Shugaban kwamitin shirya babban taron kuma gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam, ya shaidawa BBC cewa: “Mun zo mun hada kanmu; ba [rarrabuwar kawuna], ba bangare, ba komai.

“Hukumar Zabe ta aiko mana takarda—wadda na karanta a wurin wannan taron namu—ba wanda aka kora, ba zancen dakatarwa, duk wanda suke ’ya’yan jam’iyyar ne a da haka suke a yanzu”.

Sai dai irin kalaman da wadansu wadanda ake takun saka da su ke yi na nuna cewa matsalar ba ta gushe ba.

Sanata Muhammad Muhammad, daya daga cikin wadanda ke tababa a kan sahihancin kwamitin shirya babban taron, ya ce: “Mu mun dauka kwamitin shirya babban taron da jam’iyya ta nada a Maiduguri shi zai yi aiki, ba wanda daga baya Hukumar Zabe ta zo da takardar [amincewa da shi] ba”.

Ya zuwa yanzu dai gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ne kadai ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar.