ECOWAS na duba yiwuwar tura sojoji zuwa Guinea-Bissau

Kasashen ECOWAS
Image caption Kasashen ECOWAS

Shugabannin kasashen yammacin Afirka sun kammala wani taron gaggawa a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, da zummar gano hanyar warware rikice-rikicen da kasar Guinea-Bissau ke fama da su.

Bayan taron shugabannin sun ce, za a kara yin wata tattaunawar a nan gaba.

Da yake bude shawarwarin na Abuja, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce, dole kasashen yankin na yammacin Afirka su agaza wa Guinea-Bissau.

Najeriya ta bada shawarar tura kimanin sojoji 600 zuwa Guinea-Bissau.

Kungiyoyi masu fataucin miyagun kwayoyi na yankin kudancin Amirka sun yi kane-kane a kasar ta Guinea-Bissau, inda suke yada zango a kan hanyarsu ta zuwa Turai.