'Yan takarar PDP hudu za su hade wuri guda

Tutar jam'iyyar PDP
Image caption 'Yan takarar jam'iyya PDP hudu za su marawa daya baya

Yayin da a yau ake sa ran Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabacin kasar, wadansu masu son maye gurbinsa sun yanke shawarar hadewa wuri guda.

Wata sanarwa da ta fito daga kungiyoyin yakin neman zaben masu son zama ’yan takarar jam’iyyar PDP su hudu ta yi nuni da cewar sun amince su kulla wani kawancen fitar da dan takarar shugaban kasa guda daya a tsakaninsu.

A cewar sanarwar, 'yan takarar da suka amince su hada kai wajen marawa mutum guda daga cikinsu baya sun hada da tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, da gwamnan Jihar Kwara, Bukola Saraki, da Janar Aliyu Gusau.

Sanarwar, wadda ke dauke da sa hannun daraktan yakin neman zaben Janar Babangida, Cif Raymond Dokpesi, da kuma daraktan yakin neman zaben Atiku, Mista Chris Mammah, ta ce mutanen hudu za su baiwa juna cikakken hadin kai domin cimma manufa guda.

Haka nan kuma ta yaba da abin da ta kira ‘sadaukar da kai’ da mutanen hudu suka yi don cimma manufar da suka sanya a gaba.

Sanarwar ta kuma ce mutanen hudu sun bukaci magoya bayansu a fadin Najeriya su kwantar da hankulansu, suna masu tabbatar da cewa za su yi aiki tare domin ciyar da kasar gaba.

Ko wannan sanarwa za ta yi wani tasiri a zahiri?

Wannan abu ne wanda sai a ’yan kwanaki kadan masu zuwa za a gani.