An kama mutane biyar kan ziyarar Fafaroma Birtaniya

Fafaroma Benedict
Image caption Fafaroma Benedict

'Yan sandan yaki da ta'addanci sun kame mutane biyar a birnin London bisa zargin shirya kai harin ta'addanci.

Jami'ai dai na danganta kame mutanen da ziyarar da Fafaroma ya ke yi a Birtaniya.

An dauki wadanda ake zargin aiki ne a matsayin masu shara a kan titin da Fafaroman zai ziyarta a yau.

An tsare su ne a lokacin da suka je wurin aiki.

Wakilin BBC ya ce an kame mutanen biyar ne da shekarunsu suka fara daga ashirin da shida zuwa hamsin a wata cibiyar kasuwanci dake tsakiyar birnin London da karfe shidda saura kwata na safiyar yau.

'Yan sandan dai na dauke da makamai amma ba su yi harbi ba.

Sai dai 'yan sanda sun ce sun dauki kwararan matakan tsare lafiyar Fafaroman don haka babu bukatar ya sauya tsarin ziyarce-ziyarcen da zai yi.