Ra'ayi Riga: Matsalar rashin tsaro a Najeriya

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Matsalar tsaro a Najeriya matsala ce da kusan a kullum ake magana a kanta. Ko a farkon makon nan, shugaba Goodluck Jonathan ya sake jaddada muhimmancin hada karfi da karfe wajen tunkararta, inda a lokacin da yake bikin bada karin girma ga sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar, ya bukace su da su bada hadin kai ga rundunar 'yan sanda wajen shawo kan matsalar.

Shugaba Jonathan ya ce Najeriya na cikin wani yanayi mawuyaci, saboda karuwar aikata miyagun laifufuka da suka hada da sace jama'a, da fashi da makami, da aikata kisan gilla da makamantansu. Game da matsalar tsaron, a farkon makon nan ne aka kashe wasu iyalai 'yan gida daya a Kano, lamarin da 'yan sanda ke ci gaba da bincike a kansa, yayin da kuma can a Kaduna, wasu 'yan bindiga suka shiga gidan wani babban jam'in hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, suka halaka shi.

Domin tattaunawa kan matsalar rashin tsaron, mun gayyato Alhaji Abubakar Tsav, tsohon kwamishinan 'yan sandan Najeriya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro.

Akwai kuma Dokta Isma'il Zango, Malami a sashen nazarin zamantakewar dan Adam a jami'ar Bayero dake Kano.

Sai kuma Alhaji Musa Jika, shugaban kungiyar Amnesty Support Group, wata kungiya mai zaman kanta a Kaduna.

Akwai kuma masu sauraro da suka kawo tasu gudunmawar.