Ba ma keta hakkin dan-Adam sosai -Senegal

Shugaba Abdoullahi Wade na Senegal
Image caption Shugaba Abdoullahi Wade na Senegal

Hukumomi a Senegal sun amince cewa a kan ganawa mutane ukuba a kasar, amma ba sosai ba.

Gwamnatin kasar ta Senegal ta ce kasar abar misali ce wajen kare hakkin bil-Adama kuma tana hukunta duk wani jami'i da aka samu yana keta hakkokin na bil-Adama.

Wadannan kalamai na zuwa ne bayan wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta fitar, wanda ya zargi kasar da keta hakkokin bil-Adama.

Kungiyar dai ta yi bayanin irin matakan keta hakkin bil-Adaman da ta ce an yi shekara da shekaru ana aiwatarwa a kasar.

Kungiyar ta tattaro bayanai daga mutane farar hula wadanda suka yi zargin jami'an tsaro sun gana musu ukuba ta hanyar amfani da wutar lantarki da kona su da ma shake su.

A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar sadarwa ta kasar ta ce lallai hakan na faruwa amma ba sosai ba.

A cewar gwamnatin, ana gudanar da bincike don tabbatar da zarge-zargen cewa ba a hukunta jamiā€™an da ke ganawa mutane ukubar.