Valencia zai iya dawowa a watan Fabrairu

Image caption Valencia bayan da ya samu raunin

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce akwai yiwuwar dan wasansa Antonio Valencia zai dawo taka leda a watan Fabrairu bayan raunin da ya samu a wasan da kungiyar ta buga da Rangers a gasar zakarun Turai.

Dan wasan da ya karye ne a idon sahun shi kuma tuni aka yi mishi aikin tiyata.

Da farko dai likitoci sun ce dan wasan ba zai samu damar taka leda ba a kakar wasan bana, saboda munin raunin da ya samu.

Ferguson ya ce: "A baya mun samu fargabar cewa dan wasan ba zai samu taka leda ba a kakar wasan bana, saboda munin raunin da ya samu amma bayan aikin da aka yi mishi, akwai yiwuwar cewa dan wasan zai dawo taka leda a watan fabrairun badi"