Sojin Mauritania sun kara da mayakan Al-Qa'ida

Sojojin kasar Mauritania
Image caption Sojojin kasar Mauritania sun kara da Al-Qaida, reshen arewacin Afirka a kan iyakar Mauritaniar da kuma Mali

Sojojin Mauritania sun kara da mayakan kungiyar Al Qaeda, reshen arewacin Afirka, a kan iyakar Mauritaniyar da kasar Mali.

Wani jami'in sojan Mauritaniyar ya ce, mayakan Al Qaeda goma sha biyu, da dakarun Mauritaniya biyu, sun rasa rayukansu, kuma har yanzu ana cigaba da gwabzawa.

Ana tsammanin cewa, kungiyar Al Qaedan, reshen arewacin Afirka, ita ce ta sace wasu 'yan kasashen waje su bakwai a Nijar, a 'yan kwanakin nan, wadanda suka hada da Faransawa biyar.

Wasu jami'ai sun musanta cewa, akwai alaka tsakanin fadan da ake, da kuma satar mutanen.