CENI ta tsaida jadawalin zabuka na dindindin a Nijar

Shugaban mulkin Nijar Salou Djibo
Image caption Hukumar zaben Nijar ta CENI ta tsaida jadawalin zabukan kasar na dindindin

A jamhuriyar Nijar Hukumar zaben kasar mai zaman kanta, watau CENI, ta tsaida jadawalin zabe na dindindin na gudanar da zabubbukan da za su mayar da kasar a kan tafarkin demokaradiya.

Hukumar ta CENI ta ce zaben jin ra'ayin 'yan kasa a kan sabon kundin tsarin mulki, wato referendum, za a yi shi ran 31 ga watan oktoba na 2010, sannan a rantsar da sabon shugaban kasa ran 6 ga watan afrilu na 2011

Shugaban hukumar mai shara'a Ghusman Abdraman yace ya zuwa yanzu hukumar tasu ta sami miliyan 21 na kudin saifa domin gudanar da zabukan