Fafaroma ya gana da mutane 5 da aka ci zarafi

Shugaban Cocin Roman Catolika Fafaroma Benedict
Image caption Fafaroma ya gana da wasu mutane biyar da aka ci zarafi, a ziyarar da yake yi a Burtaniya

A ziyarar da yake yi a burtaniya Fafaroma Benedict ya gana da mutane biyar wadanda wasu limaman cocin catolika suka yi lalata dasu.

A wata ganawa da yayi dasu ta sirri a kudu maso yammacin landan, Fafaroma Benedict yace ya kadu game da abinda yaji kuma ya bayyana tausayinsa saboda wahalar da mutanen suka sha.

Fadar Batican dai tace Fafaroman ya sake nanata cewar cocin Roman Catholican na daukar matakai na kare kananan yara da kuma binciken zarge zargen cin zarafin.

Tun da farko dai shuagban ya nemi afuwa a bainar jama'a game da cin zarafin da wasu limaman coci cocin sukayi, yana mai bayyana cewar wani laifi ne da bama a son fada.