Dakarun Burtaniya na janyewa daga yankin Sangin

Image caption Dakarun Burtaniya a Afghanistan

Dakarun Burtaniya na janyewa daga yankin Sangin dake lardin Helmand, a Afghanistan inda dakarun Amurka ke maye gurbinsu.

Fiye da sojin Burtaniya dari ne dai aka kashe a Sangin, wato kimanin sulusin sojin Burtaniyan da suka mutu a Afghanistan a cikin shekaru taran da suka gabata.

Mahukuntan Burtaniya sun ce dakarun za su koma wani bangaren na lardin Helmand ne domin cigaba da aikinsu.

Shi dai yankin Sangin, na da matukar muhimmanci ga mayakan Taliban, kasancewar ta nan suke shigar da kayayyakin bukatansu cikin kasar.